OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

EFCC ta kama Shugaban Majalissar Dokokin jihar Ogun

EFCC ta kama Shugaban Majalissar Dokokin jihar Ogun

Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta cafke shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Olakunle Oluomo.

 Majiyoyi sun ce an kama Oluomo ne da misalin karfe 9 na safiyar yau a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

 Majiyar ta kara da cewa jami’an hukumar ta EFCC ne suka cafke shi domin ya amsa tambayoyin da suka shafi almundahanar wasu kudade.

 Kawo yanzu Shugabancin Hukumar ta EFCC ba ta tabbatar da kama dan majalisar ba  amma ana sa ran nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa.

Sai dai wata majiya a cikin Hukumar ta EFCC ta tabbatar da cewa hukumar ta gayyaci Shugaban majalisar jihar Ogun din lokuta da dama amma ya kasa amsa gayyatar.

An kai shi ofishin EFCC na birnin Legas don ci gaba da yi masa tambayoyi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci