OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Raba Auren Shekara 10 Saboda Rashin Haihuwa

Kotu Ta Raba Auren Shekara 10 Saboda Rashin Haihuwa

Wata kotun al'adu dake zamanta a Abuja ta raba auren da yakai tsawon shekara 10 saboda rashin haihuwa.

Auren da aka raban tsakanin Blossom Ameh da mijinta Simon saboda yakawo ƙarshe ne a dalilin rashin samun ƴaƴa.

Kamar yadda wani rahoto daga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, kotun al’adu da ke Nyanya, Abuja ce ta daƙile auren a ranar Juma’a.

Mai shari’a Doocivir Yawe ya kawo karshen auren ne bisa dalilin rashin samun nutsuwa a zaman auren da rashin haihuwar ya haddasa.

 “A rubuce yake cewa dukkan bangarorin biyu sun amince a raba auren sannan kuma wanda ake ƙara ya bukaci kotu da ta baiwa matarsa ​​takardar saki.
 
“Don ganin haka, kotu ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta ba mai karar takardar saki. 

"An kuma umarci wanda ya shigar da ƙara ya mayar wa wanda ake kara kuɗi Naira dubu 50,000," in ji Yawe.

Matar ​​ta kai Simon gaban kotu ne tana neman a raba auren saboda bata buƙatan ci gaba da zama dashi.

“Na gaji a wannan auren, Na yi iya ƙoƙarina don in haifi ƴaƴa amma duk ƙoƙarina ya ci tura.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci