OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan sanda sun sako Dan jaridar da suka tsare

Yan sanda sun sako Dan jaridar da suka tsare

Yan sanda sun sako dan jaridan da ke aiki da gidauniyar bincike ta FIJ, Daniel Ojukwu bayan ya wallafa wani rahoton bincike alamuran gwamnatin.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun saki Ojukwu ne a ranar Juma’a da rana bayan ya kwashe kwanaki tara a tsare.

Mamallakin FIJ, Fisayo Soyombo ya tabbatar da faruwar lamarin. Har yanzu ba'a tabbatar da wadanne irin sharuddan belin aka sanyawa Ojukwu ba.

Ojukwu ya bace ne a ranar Larabar da ta gabata tare da kashe lambobin wayarsa, hakan yasa abokan aikinsa da ‘yan uwa da abokan arziki suka fara nemansa ruwa a jallo sai da gidan jaridar FIJ suka Kai rahoton bacewarsa gurin yan sanda aka gano cewar tuntuni yana tsare a hannun su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci