OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Kogi ta dau aniyar ceto daliban CUSTEC da akayi garkuwa dasu

Gwamnatin Kogi ta dau aniyar ceto daliban CUSTEC da akayi ga

Gwamnatin jihar Kogi, ta sha alwashin ceto daliban da aka sace na jami’ar Confluence University of Science and Technology, CUSTEC, Osara, Okene, da ransu.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa Kingsley Fanwo ya fitar. Gwamnatin Kogi ta ce jami’an tsaro ciki har da mafarauta na cigaba da farautar masu garkuwa da mutanen.

Bugu da kari, gwamnatin ta kuma sha alwashin ba za ta mika wuya ga ‘yan ta’adda ba. 

A cewar sanarwar, “ana samu rahoton, gwamna Ahmed Ododo ya bukaci jami'an tsaro su bi diddigin masu garkuwa da mutanen tare da tabbatar da an kubutar da daliban da aka sace tare da cafke wadanda suka sace su. Jami’an tsaro, a halin yanzu suna ci gaba da iya bakin kokari domin tabbatar da ceto daliban da aka sace ba tare da an rasa rai ba."

“Ya zuwa yanzu, an ba da rahoton bacewar dalibai tara. Muna so mu tabbatar wa dalibai da iyaye da daukacin al’ummar jihar Kogi cewa gwamnati na kan gaba wajen ganin an ceto dukkan daliban da aka sace da ransu."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci