OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hadi Sirika da yarsa Fatima sun gurfana a gaban kotu

Hadi Sirika da yarsa Fatima sun gurfana a gaban kotu

Hadi Sirika, ministan sufurin jiragen sama a gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gabata da diyarsa Fatimah sun isa babban kotun birnin tarayya.

 

 Mutanen biyu sun bayyana a gaban kotu a safiyar ranar Alhamis domin gurfanar da su a gaban kuliya bisa zarginsu da laifin zamba na Naira biliyan 2.7. 

 

Wani faifan bidiyo da gidan talabijin na Channel TV ya watsa ya nuna wadanda ake zargin suna tattaunawa da lauyoyinsu kafin a fara shari'ar.

 

Allnews.ng ta ruwaito cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta nuna a shirye ta ke ta gurfanar da tsohon ministan, yarsa Fatimah da wasu mutane biyu. Sauran mutane biyun da ake zargin sun hada da Jalal Hamma da Al-Duraq Investment Ltd.

 

 Hukumar ta gurfanar da mutanen ne bisa zargin almundahanar Naira biliyan 2.7 da aka gano a ma’aikatar sufurin jiragen a zamani da take karkashin Sirika da gwamnatin Shugaba Buhari.

 

 Allnews.ng ta kuma ruwaito cewa hukumar EFCC ta tsare Hadi Sirika a watan Afrilu. An yi wa Sirika tambayoyi game da wasu kwangilolin da ake zargin ya amince wa Engirios Nigeria Limited, wani kamfani da kaninsa, Abubakar Sirika ke kula da shi.

 

 A watan Janairu, Festus Keyamo, ministan sufurin jiragen sama ya bayyana cewa hukumar EFCC na duba yadda Sirika ya gudanar da hada-hadar kasuwancin Nigeria Air.

 

 Wani dan majalisa mai suna Nnolim Nnaji ya bayyana kaddamar jirgin a matsayin yaudara tun a wannan lokacin.

 

 Nnaji wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin sufurin jiragen sama ya bayyana hakan yayin zaman majalisar.

 

Saidai tsohon ministan sufurin jiragen sama, Sanata Hadi Sirika, dan majalisa Nnaji ya bukaci a ba shi cin hancin kashi biyar bisa dari na kudin da aka samu a kwangilar kamfanin na Najeriya Air.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci