OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta bada umarnin kama tsahon babban Hafsan rundunar sojin ruwa

Kotu ta bada umarnin kama tsahon babban Hafsan rundunar soji

Mai shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya bayar da izinin kama tsohon babban hafsan rundunar sojin ruwa Vice Admiral Usman Jibrin, tare da wasu jami’ai guda biyu bisa zargin karkatar da kudi har Naira biliyan 1.5.

 

 Hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta, ICPC, ta gabatar da mutanen uku a gaban kotu bisa tuhumarsu da hallata kudin haram da suka kai Naira biliyan 1.5. 

 

An bayar da sammacin kamen ne biyo bayan sauraron karar da aka shigar, mai lamba FHC/ABJ/CR/158/2023, wanda lauyan ICPC Osuobeni Ekoi Akponimisingha ya shigar. 

 

A cikin karar, lauyan ya bayyana cewa, Vice Admiral Usman Jibrin Oyibe, Adam Imam Yusuf, da Birgediya Janar Ishaya Gangum Bauka, suna fuskantar bincike kan zargin halartar kudin haram da kuma bayar da bayanan karya, hadi da karkatar da kudade daga rundunar sojin su zuwa wasu kamafanoni mallakin su.

 

 Lauyan ya shaida wa kotun cewa, duk da an bayar da belin su bisa la'akari da matsayin su na ma’aikata da kuma tsofaffin jami’an gwamnati, wadanda ake tuhumar sun kasa gurfana a gaban kotu, saboda haka lauyan ya bukaci kotun da ta bayar da damar kamo su domin gurfanar da su a gaban kuliya. 

 

Wadanda ake tuhumar dai an lissafa su ne a matsayin na daya zuwa na shida a cikin tuhume-tuhume 17, da suka hada da Usman Jibrin Oyibe, Adam Imam Yusuf, Birgediya Janar Ishaya Gangum Bauka, Lahab Integrated & Multi Services Limited, Gate Coast Properties International Limited, da Ummays Hummayd Energy Ltd.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci