OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Yan Nageriya Sama Da Miliyan 100 Sunyi Rajistar Katin Dan Kasa NIN

Yan Nageriya Sama Da Miliyan 100 Sunyi Rajistar Katin Dan Ka

Hukumar Kula da katin shaidar dan Kasa, NIMC, ta ce sama da yan Najeriya miliyan 107 ne sukayi rijistar lambar shaidar dan kasa, NIN. 

Darakta Janar ta Hukumar, Odusote Cocker ce ta bayyana hakan a Abuja yayin wata ganawa da manema labarai inda ta bayyana nasarorin da ta samu a cikin shekara daya da fara jagorancin ofishin.

A cewar Cocker, an kara adadin da miliyan 3.2, daga miliyan 104 a watan Disamba 2023 zuwa miliyan 107m a yanzun.

Ta ce hukumar ta cimma wani muhimmin mataki ba wai a tsarin rajista kadai ba, har ma da sassauta tsarin, tsaftace tsarin, amfanin da sabbin fasahohi don inganta kayan aikinsu, karin yawan ma’aikata da kuma dakile masu zamba da masu karbar rashawa.

Tare da ci gaba da karuwa a cibiyoyin rajista kuma ma’aikata 3,656 Odusote ta ce tana shirin kara adadin masu rajistar zuwa miliyan 200 daga 107m don kammala rajistar nan ba da jimawa ba.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci