OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

Kotu ta dakatar da Ganduje daga shugabancin APC

APC National Chairman, Abdullahi Umar Ganduje

Babbar kotun jiha karkashin mai Shari'ah Usman Na'abba ta dakatar da tsohon gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje a matsayin dan jam'iyyar APC har zuwa kammala sauraron ƙarar da wasu yan jam'iyyar a mazabar Ganduje suka shigar a gaban kotun.

 

Mai Shari'ah Na'abba na babbar kotun ta jiha ya amince da dalilan masu ƙarar inda ya amunce da yin umarnin dakatar da shi Ganduje da kar ya sake kiran kansa shugaban APC da kuma ɗan Jam'iyyar, a takardar mai dauke da hatimi da kuma saka hannun alkali mai kwanan wata 17-4-2024.

 

Mallam Haladu Gwanjo mai baiwa APC shawara a mazabar ta Ganduje ya bayyana cewar dinga dacewar zuwa kotun ne domin neman mafita.

 

Kotun ta bayar da umarnin, Ganduje ya daina jagorantar duk wani al’amuran kwamitin gudanarwa na jamiyyar.

 

 Hukuncin da Mai Shari’a Usman Malam Na’abba ya bayar a ranar Talata ya biyo bayan karar da Dr Ibrahim Sa’ad ya shigar a madadin ‘yan majalisar zartarwa guda biyu na jam’iyyar APC a karamar hukumar Dawakin-Tofa da kuma mai shawartar 'yan jamiyyar Haladu Gwanjo.

 

Alkalin Kotun Mai shari’a Na’abba ya dakatar da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC na jihar Kano daga yin katsalandan a alamuran kwamitin mazabar Ganduje domin sun cika dukkan kaidojin da kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada kafin su dakatar da Ganduje.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa 30 ga watan Afrilun 2024.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci