OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Kotu Ta Bada Umarnin Sake Zaɓen Fidda Gwani Na Jam'iyyar PDP A Mazaɓar Abeokuta ta Arewa

Kotu Ta Bada Umarnin Sake Zaɓen Fidda Gwani Na Jam'iyyar PD

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Abeokuta, jihar Ogun, ta umarci jam’iyyar PDP da ta gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na mazabar Abeokuta ta Arewa/Obafemi-Owode da Odeda.

Kotun ta kuma bayar da umarnin cewa dole ne jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa su kula da sabon zaɓen fidda gwanin.

Wanda ya shigar da ƙarar, Abiodun-Oni Samuel Oluwafemi, ya maka jam’iyyar PDP, shugaban PDP na ƙasa;  Iyorchia Ayu, shugaban jam'iyyar PDP na jihar;  Sikirulahi Ogundele, da INEC a gaban kotu, a matsayin wadanda ake tuhuma na 1, 2, 3 da 4, suna ƙalubalantar sakamakon zaɓen fidda gwani.

Mai shigar da ƙarar ta bakin lauyansa, A. Okelola, ya caccaki jerin sunayen wakilan da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaben fidda gwani.

Da yake yanke hukuncin, mai shari’a J.O Abdulmalik ya umarci jam’iyyar da ta sake gudanar da sabon zaɓen fidda gwani na mazaɓar tarayya ta Abeokuta North/Obafemi-Owode da Odeda a cikin kwanaki 14 daga ranar da aka yanke hukuncin.

Jaridar Daily Trust tace Kotun ta kuma ba da umarnin cewa dole ne jam’iyyar ta yi amfani da jerin sunayen wakilai na asali don sake zaɓen.

Sa'annan ta ƙara da cewa ɗan takarar da yayi nasara a zaɓen fidda gwani dole hukumar zaɓe ta amince da shi.

Da yake mayar da martani, lauyan mai shigar da ƙara, A. Okelola ya yabawa bangaren shari’a kan tsayawa kan turbar gaskiya da adalci.

Ya ce a ƙarƙashin tsarin dimokuradiyya, dole ne a samar da daidaito a kuma bai wa kowa damar shiga ba tare da tauye haƙƙin kowa ba.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci