OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Kotu ta bada belin Cubana Chief Priest akan kudi N10M

Kotu ta bada belin Cubana Chief Priest akan kudi N10M

Cubana Chief Priest

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Legas, a ranar Laraba, ta bayar da belin Pascal Okechukwu, wanda aka fi sani da Cubana Chief Priest kan kudi N10m.

 

Tun da fari dai shahararren dan kasuwar ya ki amsa laifin da aka tuhume shi dashi na cin zarafin naira a lokacin da ake shari’ar.

 

An gurfanar da Cubana a gaban mai shari’a Kehinde Ogundare bisa tuhume-tuhume guda uku da suka shafi cin zarafin Naira ta hanyar yin likin N500,00 a wani taro a Eko otal wanda ya saba da dokar babban bankin kasa CBN ta 2007.

Hukumar EFCC dai ta dauki aniyar hukunta dukkan wanda aka samu da laifin wulakanta Naira a kasarnan.

Idan za'a iya tunawa Mai shari’a Abimbola Awogboro na babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas a ranar Juma’ar da ta gabata 12 ga watan Afrilu ta yanke hukuncin daurin watanni 6 a gidan kaso ba tare da zabin tara ba ga Bobrisky wanda hukumar EFCC kan tuhume-tuhume shida da suka hada da wulakanta Naira.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci