OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jami’an Ƴan Sanda 389 Ne Suka Mutu a Borno Yayin Yaƙi Da Boko Haram

Jami’an Ƴan Sanda 389 Ne Suka Mutu a Borno Yayin Yaƙi Da

Nigerian Police force

Rundunar ƴan sanda ta ce aƙalla jami’an ta 389 ne suka mutu a fada da ƴan ta’addan Boko Haram a jihar Borno cikin shekaru 11 da suka gabata.

Jihar Borno dai na ɗaya daga cikin jihohin arewa maso gabas da suka fi fama da matsalar tashe-tashen hankula da aka kwashe shekaru goma ana yi a Najeriya.

Lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare da raba wasu da dama da muhallansu.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Abdu Umar ne yayi wannan jawabi yayin ƙaddamar da sabon ofishin ƴan sanda da barikin da aka gina a Beneshiek, hedkwatar karamar hukumar Kaga ta jihar.

Kwamishinan ya ce aƙalla wasu 450 sun jikkata a yakin da ake yaƙi da ƴan ta’addan.

A cewar CP, sama da barikokin ƴan sanda 24 da ofisoshin su 30 ne aka ƙona aka kuma an lalata su, yayin da ƴan ta’addan suka kwashe wasu kayan aiki.

"Idan za'a iya tunawa a lokacin da ƴan ta’addan suke kan kaifinsu tsakanin shekarar 2011 zuwa yau, sama da ofisoshin ƴan sanda 30 da barikin ƴan sanda 24 ne ƴan ta’addan suka ƙona ko kuma suka lalata su,” inji shi.

"Yan sanda 389 ne suka rasa rayukansu, sama da ƴan sanda 450 suka jikkata.

"Yayin da aka ƙona kayan yaki da laifuka da ƴan ta'addan da dama, cewar Jaridar Vanguard.

"Asarar da rundunar ƴan sandan jihar Borno ta samu ya jawo ɗaukar matakai da dama, wanda a yau muna ganin ɗaya daga cikin irin wadannan matakan.”

Umar ya yabawa ƙoƙarin Gwamna Babagana Zulum na sake gina wasu ofisoshin ƴan sanda da aka lalata a fadin jihar.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci