OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Amurka bazata halarci bikin rantsar da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ba

Amurka bazata halarci bikin rantsar da shugaban kasar Rasha

Russian President Vladimir Putin

Gwamnatin Amurka ta ce ba zata halarci bikin rantsar da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin a yau Talata ba.

 

 Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya shaidawa manema labarai jiya litinin cewa "ba za mu tura wakili bikin rantsar da shi ba." 

 

Da aka tambaye shi ko kauracewa bikin na nufin Amurka ta dauki Putin a matsayin harramtaccen shugaba, Miller ya ce: "Ba mu yarda da sahihancib zaben ba amma shi ne shugaban kasar Rasha kuma zai ci gaba mulki." 

 

Putin, mai shekaru 71, ya jagoranci Rasha a matsayin shugaban kasa ko kuma firaminista tun farkon karni. 

 

Hukumar zaben kasar ta ce a watan Maris din da ya gabata ne ya lashe wa'adi na biyar da kashi 87.28 na kuri'un da aka kada.

 

Idan za'a iya tunawa babban mai sukar Putin, Alexei Navalny, ya mutu a gidan yarin Arctic a watan Fabrairu. Matarsa Yulia Navalnaya, ta shawarci kasashen duniya da kada su amince da Putin a matsayin halastaccen shugaba. 

 

Za a rantsar da shi kan karagar mulki a wani gagarumin biki da za a yi a Kremlin ranar Talata, inda zai shiga wani wa'adi na biyar mai cike da tarihi. Za a nuna bikin kaddamarwar kai tsaye a galibin manyan gidajen talabijin na Rasha daga tsakar rana (0900 GMT), lokacin da ayarin motocin alfarma za su tuka Putin zuwa fadar Grand Kremlin ta Moscow. Bayan isowarsa, zai bi ta hanyoyin fadar zuwa babban dakin taro na Saint Andrew, inda zai yi rantsuwar shugaban kasa tare da yin takaitaccen jawabi ga 'yan kasar Rasha. 

 

An gayyaci jami'an gwamnati da jami'an diflomasiyyar kasashen waje zuwa birnin Moscow, ciki har da jakadan Faransa Pierre Levy, wanda ake sa ran zai halarta.

 

Sauran kasashen Turai da suka hada da Poland da Jamus da Jamhuriyar Czech sun yi nuni da cewa ba za su aika da wakilai ba a yayin da ake takun-saka kan batun rikicin Rasha da Ukraine.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci