OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamna Zulum yayi alhinin mutuwar mai bashi shawara Kester Ogualili

Gwamna Zulum yayi alhinin mutuwar mai bashi shawara Kester O

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya yi alhinin rasuwar mai bashi shawara na musamman kan hulda da jama’a, Cif Kester Ogualili, inda ya bayyana shi a matsayin mai kawo zaman lafiya kuma jakadan kabilar Igbo a jihar. 

Gwamnan wanda ya bayyana bakin cikinsa yace marigayin ya yi wa al’ummar jihar Borno hidima sosai tsawon shekaru. 

Marigayi Ogualili ya rasu ne a ranar Juma’a da rana a asibitin koyarwa na Jami’ar Maiduguri bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Gwamna Zulum a cikin wani sako da babban hadiminsa Abdurrahman Ahmed Bundi ya fitar ya jajantawa iyalan marigayi Ogualili, abokansa da kuma Zenith Bank plc, inda marigayin ya yi aiki na tsawon shekaru.

Zulum ya ce “Na yi bakin ciki da rasuwar Hon Kester Ogualili, ya yi wa mutanen Borno hidima tsawon shekaru. Hon. Kester ya kasance mai karfafa zaman lafiya kuma jakadan kabilar Igbo a Borno.

"Za mu ci gaba da tunawa da rawar da ya taka don samar da zaman lafiya a tsakanin alumma."

Gwamnan ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan marigayin, ya kuma baiwa iyalansa hakurin jure rashin.

Marigayi Ogualili ya fito ne daga karamar hukumar Dunukofia ta jihar Anambra kuma ya gudanar da mafi yawan rayuwarsa a jihar Borno.

Ya taba rike mukamin mai ba da shawara na musamman kan hulda da jama’a a karkashin gwamnatin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima lokacin yana gwamnan jihar Borno a tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019, sannan daga bisani gwamnatin Zulum a irin wannan mukami daga 2019 zuwa 2023 aka sake nada shi a watan Janairun 2024.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci