OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Harsashin bindiga yayiwa wani Dan jarida rauni a gidan gwamnatin Kano

Harsashin bindiga yayiwa wani Dan jarida rauni a gidan gwamn

Harsashin bindiga a fadar gwamnatin Kano ya jikkata wani Dan jarida Naziru Idris Ya'u dake aikin da gidan talabijin din ARTV a jihar.

 

Lamarin faru ne a daren jiya juma’a a fadar gwamnatin Kano da misalin 6:30 na yamma kamar yadda wani gidan rediyo ya rawaito.

 

Dan jaridar dake aiki da gidan talabijin na jihar Kano ARTV mai suna Nazirun Idris Ya'u ya tabbatarwa da faruwar lamarin, sai dai ya ce ba’a san daga inda aka harbo harsashin bindigar ba.

 

Naziru Idris ya ce suna tsaye kusa da masallaci a harabar gidan gwamnatin Kanon kawai yaji saukar harsashin bindigar ya soke shi a hannu daya duba yaga harsashin sai ya sa daya hannun ya zare shi.

 

Ya kara da cewa harsashin ya masa rauni amma ba mai yawa ba, kuma tuni jami’an yan sanda a fadar gwamnatin Kano suka kadamar da bincike kan lamarin.

 

Kawo yanzu fadar gwamnatin Kano da rundunar yan sandan ba su ce komai ba kan wannan harbin bindiga da ya shafi dan jarida a fadar gwamnatin Kano.

 

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar kare haƙƙin Ɗan'adam ta majalisar ɗinkin Duniya ta bayyana shekara ta 2023, a matsayin mafi muni ga yan jarida.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci