OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Katsina ta sanya sama da biliyan uku a fannin kiwon lafiya

Gwamnatin Katsina ta sanya sama da biliyan uku a fannin kiwo

Gov. Umar Dikko Radda

Gwamnatin Jihar Katsina ta ware Naira Biliyan 3.77 tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Afrilu 2024 ga bangaren kiwon lafiya. 

 

Gwamna Dikko Radda ne ya bayyana hakan a yayin taron kaddamar da majalisar jiha kan harkokin lafiya da aka gudanar a Katsina ranar Litinin.

 

 Mai taken “Gina Tsarin Kiwon Lafiya a Jihar Katsina: Kalubale, Dama da Magani,” taron majalisar ya jaddada kudirin jihar na magance matsalolin kiwon lafiya a jihar baki daya.

 

Gwamna Radda ya bayyana sunyi karin kashi 800 na kudaden da ake ware wa fannin kiwon lafiya. 

 

 “A kokarin mu na cika alkawarin da muka daukarwa al’ummar jihar Katsina mun kara yawan kudaden da muke bayarwa ga fannin lafiya da kashi 800 cikin 100, wanda ya kai Naira biliyan 3.77 tsakanin watan Yuni 2023 zuwa Afrilu 2024,” in ji Radda.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci