OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

IPMAN Ta Janye Batun Siyar Da Man Detur Kan N180

IPMAN Ta Janye Batun Siyar Da Man Detur Kan N180

Kungiyar masu dillancin man fetur ta kasa, IPMAN ta sanar da janye batun siyar da litar mai daga naira 180 zuwa sama.

A zantawar sa da manema Labarai a birnin tarayya Abuja, Shugaban Kungiyar, Chinedu Okoronkwo yace kungiyar za ta ci gaba da siyar da shi a kan farashin gwamnati na naira 165 bayan cimma matsaya da hukumar PPMC.

Okoronkwo ya kara da cewa yanzu haka ana loda man daga Legas zuwa sauran yankunan kasar nan, kuma yana sa ran nan gaba kadan za a daina dogayen layuka a gidajen man a fadin kasar.

Ya bukaci yan Najeriya da su kwantar da hankulan su, domin za su ci gaba da samun man fetur din a farashin 165.

A baya IPMAN reshen jihar Legas ta bayyana cewa ba za ta iya sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita, bayan da ta ce yanayin yadda take kashe kudi kafin sauke man a gidaje ya karu sosai.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci