OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Katsina ta rufe gidajen Man fetur da suke sayarwa yan ta'adda man fetur

Gwamnatin Katsina ta rufe gidajen Man fetur da suke sayarwa

Gwamnatin jihar Katsina ta rufe gidajen mai guda uku da ake zargi da sayarwa ‘yan ta'addan da suka addabi yankin man fetur. 

Kwamitin shawo kan matsalar boye abinci da karin farashin kayan abinci ne suka rufe gidajen sayar da man fetur din.

Shugaban kwamitin, Jabiru Salisu Tsauri, da yake zantawa da manema labarai bayan rufewar ya bayyana cewa kwamitin na da hurumin tsare wadanda ake tuhuma har na tsawon sa’o’i 48 kafin a fara shari’ar.

Jabiru Salisu wanda kuma yake rike da mukamin shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin Katsina ya ce sun samu bayanan sirrin da ya tabbatar da gidajen man fetur din uku suna sayar wa yan ta'adda man fetur da tsakar dare ko da asubahin fari. 

Sai dai daya daga cikin wadanda aka rufewa gidan man ya musanta zargin da ake masa. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci