OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin tarayya ta amince wa masu matatun man fetur su sayi danyen mai da Naira

Gwamnatin tarayya ta amince wa masu matatun man fetur su say

Gwamnatin tarayya ta amince da bukatun masu matatun man fetur kamar su Dangote Refinery da Petrochemical Plant da sauran masu matatun mai a kasar nan ta hanyar ba su damar su sayi danyen man fetur da Naira maimakon Dala.

 

Hukumar kula da hadahadar man fetur ta kasa (NUPRC) ce ta sanar da sabon matakin a wani taron masu ruwa da tsaki da aka yi a Abuja, inda ta kaddamar da sabon tsarin samar da danyen mai ga matatun cikin gida. 

 

Idan za a iya tunawa, kungiyar masu sarrafa danyen mai ta kasa ta dade tana kara matsa lamba ga gwamnatin tarayya kan batun neman a sayar musu da danyen mai a kudin cikin gida wato Naira saboda suna fuskantar kalubale wajen samun Dala wanda ke barazana ga sana'arsu.

 

Sakataren Yada Labarai na kungiyar, Eche Idoko ya koka kan yadda a halin yanzu siyan danyen mai a dala shine babban kalubalen da ke fuskantar matatun man fetur yayin da ya bayyana cewa suna sayen danyen mai da dala suna sayar da man fetur din da suka tace a naira wanda babban kalubale ne.

 

“Mun nemi a sayar mana da danyen mai a naira idan akayi hakan za a rage matsin lamba a kan Naira kuma hakan zai sa disel ɗin namu ya yi arha. Kuma zai jawo hankalin masu zaba hannun jari su shigo harkar Idan aka daina amfani da kudaden waje a hada hadar man fetur zai taimaka wa darajar Naira da kashi 60 cikin 100,” inji shi. 

 

Da yake mayar da martani kan hakan a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, Babban Jami’in Hukumar NUPRC, Engr Gbenga Komolafe ya bayyana cewa bisa tanadin sashe na 109(2) na dokar masana’antar man fetur ta 2021, NUPRC ta ɓullo da wani jadawalin da zai jagoranci hada hadar danyen man fetur wanda dukkan masu ruwa da tsaki suka sanyawa hannu 

 

Komolafe ya bayyana cewa, kamar yadda aka amince da shi a cikin sabon tsarin, biyan kudin danyen man zai kasance ko dai a naira ko dala, inda ya kara da cewa hada-hadar naira za ta rage ta'allaka da akai akan kudin kasar wajen.

 

Shugaban NUPRC ya kuma yi nuni da cewa samfurin ya yi tasiri saboda dukkan bangarorin da suka dace sunyi amanna da shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci