OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Rundunar sojin ruwa ta lalata haramtattun matatun man fetur 60 a Neja Delta

Rundunar sojin ruwa ta lalata haramtattun matatun man fetur

Rundunar sojin ruwan Najeriya ta lalata haramtattun matatun man fetur 60 a yankin Niger Delta a tsakanin watan Janairu zuwa Afrilu na shekarar 2024. 

 

Kwamandan Rundunar Sojin Ruwa ta Gabas (ENC), Rear Admiral Saheed Akinwande ya kuma bayyana cewa sun kama tare da lalata kimanin lita 293,900 na AGO da aka tace ba bisa ka'ida ba a tsawon lokacin. 

 

Da yake wa manema labarai a ofishinsa da ke Calabar, Saheed Akinwande ya kuma bayyana cewa sun kwato lita 412,000 na danyen man da aka sace. 

Ya Kara da cewa " rundunar Operation Delta Sanity ya sami gagarumun nasarori tun bayan kaddamar da ita a watan Janairun bana. Wasu daga cikin nasarorin sun hada da karin lokacin sintiri na teku daga sa'o'i 1,752 zuwa jumular kimanin sa'o'i 45,540 da 30 a fadin sansanonin ta jiragen ruwa wanda ya haifar da kama mutane da dama, da lalata wasu kwale-kwalen da ake fasakauri da su hadi da kama kayan aikin da haramtattun matatun man fetur ke amfani da su" in ji shi.

 

Sakamakon yadda rundunar sojin ruwa ta dauki tsauraran matakai na yaki da ta’ammali da man fetir ba bisa ka’ida ba, an samu karuwar adadin hako danyen mai da kashi 5.85 daga 1.55mbpd zuwa 1.64mbpd kamar yadda Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya ta shaida. 

 

Manufofin aiki na OP Delta Sanity shine dakile ayyukan fasa bututun mai ba bisa ka'ida ba da sauran laifuka a yankin Neja Delta na kasar.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci