OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NSCDC ta Cafke Dalibi Da Zargin Garkuwa Da Shugaban Kwaleji a Jihar Neja

Rundunar hukumar tsaro ta farin kaya ta Civil Defense reshen jihar Neja, ta kama wani dalibi sakamakon yunkurin yin garkuwa da shugaban kwalejin koyar da kimiyar noman kifi a Jihar. 

A ta bakin mai magana da yawun rundunar, ASC Nasir Abdullahi, ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar goma ga watan Agusta na shekarar 2022.

ASC Abdullahi, ya kara da cewa wanda ake zargin, ya hada baki ne da abokan sa wadanda a halin yanzu ke boye, domin yin garkuwa da shugaban kwalejin ta hanyar rubuta masa wasika tare da yi masa barazanar biyan kudin fansa.

Kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ta bayyana, Kakakin rundunar, ya ce hukumar su, ta samu zarafin kame wanda ake zargi da laifin ne da kuma gurfanar dashi a gaban kotun majistre dake jihar Neja, kafin tatsar kudi daga hannun shugaban kwalejin makarantar su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci