OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Hukumar Kula da hakkin mai saye zata toshe manhajojin bada lamuni na intanet

Hukumar Kula da hakkin mai saye zata toshe manhajojin bada l

Hukumar kula da hakkin mai saye ta tarayya, FCCPC, ta ce za ta fara aikin toshe manhajojin lamuni da ke addabar kwastomominsu.

 

 Mukaddashin shugaban hukumar, Adamu Abdullahi, wanda ya bayyana haka a wata hira da BBC a ranar Asabar, ya ce hukumar ta fara magance matsalar cin zarafin kwastomomin da manhajojin bada bashi sukeyi a duk sanda suka gaza biyansu.

 

 “Ba da jimawa ba zai zama tarihi a kasar nan inda zakaga manhajar da wasu ‘yan Najeriya ke samun bashi cikin gaggawa don magance matsalolin dake gabansu, idan ba su biya kan lokaci ba, wasu daga cikin wadannan kamfanonin lamuni sai sun fara tura saƙonni tare da hotuna marassa dadi ga duk abokan hulɗar su.

 

 “Wannan tsangwama ya haifar da matsaloli da dama a Najeriya, domin wasu ma sun rasa ayyukansu saboda kunya ba mu yarda da irin wannan hali ba saboda ana cin zarafin kwastomomi, duk da cewa ba matsalarmu ba ce kai tsaye. Mun hada da CBN, NITDA, EFCC da kuma hukumar kare hakkin dan Adam domin kafa wani kwamiti don magance matsalar, tunda mun gano cewa suna aiki a yanar gizo kuma ba su da ofisoshi na zahiri sai muka tuntubi Google da Apple domin mu kwace manhajar duk Wanda ya karya ka'ida komai. Mun kuma hada kai da CBN domin mu toshe duk wani asusun ajiyar su,” inji shi. 

 

Shugaban na FCCPC ya bayyana cewa bayan rufe asusun, hukumar ta tuntubi manhajojin ta ba su fom din da za su cike dukkan bayanansu, adireshi, da sunan daraktocisu kafin ta ba su sabbin ka’idojin yadda za su yi aiki.

 

 “Don haka duk lokacin da muka samu koke daga kowane kwastomomi, za mu sake toshe su,” in ji shi. 

 

A yanzu, mun yi musu gargadi, kuma sun fara wannan aikin a makon jiya Litinin. 

 

Abdullahi ya kara da cewa "Sun amince a rubuce cewa ba za su sake yin amfani da damar su wajen yin kutse cikin jerin mutanen da kwastomomin su suke hulda dasu da hotunan su, don haka idan muka sake jin sun sake yin hakan, za mu rufe su nan take."

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci