OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

EFCC ta magantu kan rahoton jerin gwamnatin da ake zargi da almundahana

EFCC ta magantu kan rahoton jerin gwamnatin da ake zargi da

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta nesanta kanta da wani rahoto da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa hukumar ta fitar da jerin sunayen tsofaffin gwamnoni da suka yi almundahana.

 A wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar a ranar Lahadin nan ta bukaci jama’a su yi watsi da rahoton, inda ta bayyana shi a matsayin labarin kanzon kurege.

Hukumar ta kuma bukaci kafafen yada labarai da su tabbatar da bin diddigin bayanai daga hukumar domin gujewa yada labarin karya ga jama’a.

Ta kara da cewa hukumar ba ta fitar da jerin sunayen da ake zargin ba, ba ta kuma tattauna kan binciken tsofaffin gwamnoni da wata kafar yada labarai ba. 

Sanarwar a wani bangare na cewa: “Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, na ganin ya zama dole ta nesanta kan ta daga wani rahoto da ke yawo a sassan kafafen yada labarai na cewa ta fitar da cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnonin da ake bincike kan zargin almundahana.” Rahoton. Mai taken: "EFCC ta fitar da cikakken jerin sunayen tsofaffin gwamnoni 58 da suka wawure Naira Tiriliyan 2.187", a yake yawo a kafafen yada labarai karya ne kuma bashi da tushe domin hukumar ba ta fitar da wannan jerin sunayen ba.

"Muna umurtar jama'a da su yi watsi da rahoton domin karya ne da yaudara. Hakazalika mun shawarci kafofin yada labarai da su yi ƙoƙari su binciko bayanan da kyau kafin su yada"

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci