OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Wata da ya shude

An kama masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba 30 a jihar Neja

An kama masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba 30 a jihar Ne

Kwamishinan ma’adanai na jihar Neja, Garba Sabo, ya bayyana an kama mutane 30 bisa laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a jihar.

 

 Sabo ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Minna, inda ya ce ma’aikatar tana cigaba da bincike a kan kamfanonin hakar ma’adanai 229 domin tantance wadanda za a amince da su ko akasin hakan.

 

Ya ce an kama mutanen ne yayin wata ziyarar ba zata da ya kai wasu haramtattun wuraren hakar ma’adanai.

 

Garba Sabo yace da yawa daga cikin masu hakar ma'adanan sun tsere da suka hango zuwan jami'an tsaro.

 

Kwamishinan, wanda ya sake nanata cewa dokar hana hako ma’adanai ba bisa ka’ida ba tana nan daram a jihar, ya ce: “Ba daidai ba ne a zarge mu da rashin gudanar da aiki alhalin ba ku sanya ido kunga kokarin da muka yi ba. Mukan shiga wadannan wuraren da ake hakar ma’adinai duk da muna tare da jami’an tsaro, yawanci ana kai mana hari. Muna yin iya bakin ƙoƙarinmu don dakatar da wannan danyen aikin da bata gari suke yi" 

 

Kwamishinan ya bayyana cewar ma’aikatar tana kokarin samar da na’urar tantancewa zanen danyatsan dukkan masu hakar ma'adanai a jihar domin samun cikakkun bayanai na dukkan masu hakar ma’adinai a jihar don kawo karshen mamaye harkar da wasu yan tsirarun kamfanoni ke yi.

 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci