OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Jama'an DSS sun rufe wani asibiti a Filato

Jama'an DSS sun rufe wani asibiti a Filato

Jami’an tsaro na farin kaya DSS sun rufe asibitin Al-Ihsan dake Ungwan Rogo a Jos ta Arewa karamar hukumar jihar Filato a ranar Lahadi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito, DSS sun Rufe asibitin bisa zargin ma'aikatan asibitin da rashin kwarewa da yayi sanadiyar mutuwar wata mata.

Rahotanni sun ce wata mata ta mutu a asibitin a makon da ya gabata bayan wani tiyata da ake zargin wani Mista Lukuma Abdul ya yi mata.

Lamarin dai ya janyo cecekuce, Al'ummar yankin sun danganta rasuwar ta da aikin da akai mata saidai likitan ya musanta zargin da ake masa, yana mai cewa ba aikin da aka yi ba ne ya jawo mutuwar ta. 

Wasu daga cikin al’ummar yankin sun kai kara ga ma’aikatar lafiya ta jihar bisa zargin tafka ta’asa da aka yi a asibitin, lamarin da ya sa jami’an tsaro na farin kaya DSS suka rufe asibitin.

Wani mazaunin yankin Sadis Muhammad Albasu, ya bayyana cewa, “an dade ana zargin likitan da rashin kwarewa Amman abun bai fito filin karara ba sai bayan mutuwar matar bayan an mata tiyata"

Sadis Muhammad ya kara da cewa “Batun gaskiya shine Malam Lukman ba kwararren likita bane don haka ba shi da cancantar cancantar yin aikin tiyata. Jama’a da dama na korafi akansa, shi ya sa aka kai rahoto ga ma’aikatar lafiya ta jihar domin daukar matakan da suka dace. Shi ba likita ba ne. A halin yanzu yana makaranta amma yana gudanar da aikin tiyata a cikin al’umma" 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci