OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NSCDC ta amince da kamfanonin tsaro 1,200, ta janye rajistar 100

Hukumar NSCDC ta amince da kamfanonin tsaro 1,200, ta janye

Photo Source: Jobadung

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC) ta amince da bada lasisi ga wasu kamfanonin tsaro masu zaman kansu 1,200 tare da kashe rajistar sama da 100 a fadin kasar.

Kwamandan rundunar, Dr Ahmed Audi ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi a Abuja.

Audi ya bayyana cewa, hukumar NSCDC ta samar da tsauraran matakai na tafiyar da kamfanonin tsaro masu zaman kan su a kasar.

A cewar sa, NSCDC ta horar da kuma kula da ayyukan wasu Kamfanoni masu zaman kansu (PGC) tare da fatan samun karin horo daga yanzu zuwa karshen shekara.

Ya lura cewa sama da PGC 4,000 ne Hukumar NSCDC ta horar da su.

A wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), Audi ya kara da cewa: “Tsakanin yanzu zuwa karshen shekara, rundunar za ta horar da karin jami’ai 3,000 zuwa 4,000 ga kamfanonin masu gadi masu zaman kan su.”

“Mun sami dalilai na janye lasisin wasu da yawa saboda muna sa ido, ba da lasisi, tsarawa, horar da su da kuma kula da su.

“Mun rufe kusan 100 daga cikin irin wadannan kamfanoni wadanda saboda wani dalilin ko kuma ba sa iya aiki. 

"Muna rufe su har sai sun warware matsalolin kafin mu bude su mu ba su damar yin aiki," in ji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci