OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar NSCDC Ta Kori Ma'aikata 15 Tare Da Ragewa 9 Matsayi

Hukumar NSCDC Ta Kori Ma'aikata 15 Tare Da Ragewa 9 Matsayi

NSCDC boss, Ahmed Abubakar Audi

Shugaban Hukumar farin kaya Ahmed Audi ya bayyana cewa an sallami 15 daga cikin jamian su sannan kuma an rage ma wasu daga cikin su matsayi.

 

Bakwai daga cikin su kuma an dakatar da su, tara kuma an sanya su yin ritayar dole yayin da daya kuma aka rage masa matsayi.

 

Shugaban Hukumar ne ya sanar da mataki cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar, Olusola Odumosu, ranar Litinin a Abuja.

 

Ya ce matakin ladabtarwar ya samu amincewar hukumar tsaro ta Civil Defence, gyaran fuska, kashe gobara da hukumar shige da fice.

 

Audi ya bayyana cewa an hukunta jamian ne bisa laifukan da suka hada da sa hada baki, karbar kudi, Sa hannu na jabu, rashin gaskiya da zagon kasa ga tattalin arziki da dai sauransu.

 

Wadanda aka kora sun hada da Mataimakin Sufeto na Corps I Mataimakin Babban Jamiin Hukumar guda biyu, Mataimakin Sufeto na Corps su uku, AIC, Mataimakin Corps uku, CAIII, CAII biyu, CAII daya, Insifeto Corps daya da AIC daya.

 

Jamian da aka dakatar sun hada da mataimakan kwamandoji biyu, mataimakin kwamandan rundunar guda uku, mataimakin Sufeto na Corps II da CAII daya.

 

Ya kara da cewa "Hukumar ta kuma amince da dakatar da wani Sufeto na Corps (IC) da kuma rage IC guda daya," in ji shi.

 

Hukumar ta CG ta ci gaba da cewa matakin ladabtarwar wani bangare ne na kokarin kawar da miyagu da kuma tabbatar da ladabtarwa.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci