OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Jigawa: Dan Shekaru 10 Ya Nutse a Ruwa

Jigawa: Dan Shekaru 10 Ya Nutse a Ruwa

Drown

Wani yaro dan shekaru goma ya nutse a cikin ruwa a karamar hukumar Buji ta Jihar Jigawa wanda hakan yayi sanadiyar mutuwar sa. 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Hukumar Tsaro ta Farin kaya (NSCDC), CS Adamu Shehu ya fitar ranar Lahadi a Dutse, babban birnin jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ajali ne ya yi kiran yaron wanda ya tafi wanka a rafi tare da abokan sa a kauyen Lelen Kudu a ranar Asabar.

Shehu ya ce an tsamo gawar yaron bayan kusan sa’a biyu da nutsewa, wanda wani likita ya tabbatar da mutuwar sa. 

Mai magana da yawun hukumar,  ya gargadi iyaye da su ja kunnen ’ya’yan su a kan hatsarin da ke tattare da zuwa wanka a rafi musamman a wannan lokaci na damina da  kududdufai suka ciko. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci