OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Zaben 2023: Civil Defence Za Ta Baza Jami'ai 30,000

Zaben 2023: Civil Defence Za Ta Baza Jami'ai 30,000

Hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC, za ta baza jami’anta 30,000 domin tabbatar da zaman lafiya yayin babban zabe mai zuwa na 2023.

 

 Za'a fara gudanar da babban zaben kasar ne a ranar 25 ga watan Fabrairun shekara mai zuwa, lokacin da za a zabi shugaban kasa da mataimakinsa.

 

 Da yake jawabi yayin babban taron da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya gudanar a Abuja a ranar Lahadi, Kwamanda Janar na NSCDC, Ahmed Audi, ya ce za a baza jami’an ne a sassa daban-daban a fadin kasar domin wanzar da zaman lafiya.

 

 A cewarsa, hukumar ta NSCDC ta kammala shirye-shiryen tura duk wani abu da ake bukata domin samar da tsaro a lokacin zabe.

 

 “Rundunar ta shirya tsaf, kuma a shirye take ta yi amfani da dukkan makaman da ake bukata domin samar da tsaro yayin zaben. Muna da ma'aikata sama da 30,000 da suke kan aiki a halin yanzu kuma za mu tura wasu idan lokacin zaben ya yi" inji shi.

 

 Mista Audi ya kara da cewa, rundunar ta kammala shirye-shiryen fara taron karawa juna sani a watan Oktoba domin tattaunawa kan shirin kungiyar na tunkarar babban zaben.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci