OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

NSCDC Ta Kafa Rundunar Mata Don Kare Makarantun Najeriya 81,000 Da Ke Fuskantar Hare-Hare

NSCDC Ta Kafa Rundunar Mata Don Kare Makarantun Najeriya 81,

NSCDC boss, Ahmed Abubakar Audi

Babban kwamandan hukumar tsaron farin kaya ta kasa NSCDC Ahmed Audi, ya ce an kafa tawagar mata domin samar da tsaro ga wasu makarantu 81,000 da aka gano zasu fuskanci harin Yan ta'adda a fadin kasar nan.

 

 Ahmed Audi ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN a Abuja.

 

 Ya ce an kafa tawagar matan ne bayan an yi nazari sosai kan dukkan makarantun kasar.

 

 “Mun gudanar da gwajin tantance masu rauni wanda wani nau’i ne na bincike da muka samar domin a gano adadin makarantun da suke cikin hadari."

 

 “Bayan da muka yi wannan binciken, mun fahimci cewa akwai matsala a kasar nan ta fuskar tsaro a makarantu domin bayanan da muka samu sun ban mamaki matuka".

 

Ya kara da cewa rundunar ta bullo da wata kungiya mai suna School Community Security Vanguard, wadda ta hada malamai, dalibai, kungiyar malamai da iyaye, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma domin wayar da kan alumma game da amfanin sa Ido akan abubuwan dake faruwa a muhallin su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci