OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Legas: Hukumar NDLEA Na Neman Wani Mai Safara Kwayoyi Ruwa A Jallo

Legas: Hukumar NDLEA Na Neman Wani Mai Safara Kwayoyi Ruwa A

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta bayyana cewa tana neman wani dan jihar Legas mai suna Ademola Kazeem wanda aka fi sani da Alhaji Abdallah Kazeem Muhammed bisa laifukan da suka shafi safarar miyagun kwayoyi.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi, ya fitar ranar Talata.

 

Wanda ake neman shine mallakin Otal din Adekaz.

 

Hukumar ta ce sun ayyana neman shi ne bayan da ya kasa amsa gayyatar da suka yi masa.

 

Sanarwar ta kara da cewa, "An gano wanda ake neman shi ne ke daukar nauyin wasu masu fataucin da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kama a yunkurinsu na fitar da hodar iblis zuwa Dubai, da sauran kasashen wajen Najeriya," in ji sanarwar.

 

Ba a jima da kama hadiminsa Bolujoko Muviwa Babalola, direban BRT Legas a ranar 27 ga watan Yuni a filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport, MIA, Ikeja, Alhaji Ademola Kazeem wanda shi ne Shugaban Kamfanin Adekaz Global Integrated Services ya yi batan damo.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci