OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kaduna Tace Gobara 20 Aka Yi a Watan Agusta

Hukumar Kashe Gobara Ta Jihar Kaduna Tace Gobara 20 Aka Yi a

Fire incident

Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta bayyana cewa akalla gobara 20 ne aka samu da kuma mutuwar mutum daya a cikin watan Agusta a fadin jihar.

Daraktan hukumar kashe gobara na jihar, Paul Aboi ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata a Kaduna.

Ya bayyana cewa, mutum daya kuma ya samu raunukan gobara yayin da aka ceto daya ba tare da jin rauni ba a tsawon lokacin.

Ya bayyana cewa an samu rahoton afkuwar bala’in a Zariya, Kafanchan da cikin Kaduna.

A cewar sa: “An kubutar da kadarorin da darajar su ta kai N171,000 daga lalacewa a cikin wannan lokaci yayin da dukiyoyin N30,000 suka lalace.”

Ya kara da cewa bala’in gobara a jihar ya ragu bayan wayar wa 'yan gari kai da kuma ruwan sama mai karfi a watan Agusta.

Yayin da yake lura da cewa mafi yawan bala'in gobara na faruwa ne sakamakon rashin wutar lantarki, ya ce kashi 70 cikin 100 na faruwa ne sakamakon rashin kulawar magidanta.

Ya kuma yi kira ga gwamnan jihar, Malam Nasir El-Rufa’i da ya wadata dukkanin kananan hukumomin jihar da kayayyakin kashe gobara yayin da ya bukaci mazauna yankin su mallaki na’urorin kashe gobara a gidajen su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci