OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar EFCC Ta Kama Mutane 2,781 Bisa Laifuka Mabanbanta

Hukumar EFCC Ta Kama Mutane 2,781 Bisa Laifuka Mabanbanta

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa

Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce hukumar ta kama mutane 2,781 a ranar 24 ga watan Oktoba bisa laifi mabanbanta.

 

Bawa ya bayyana haka ne a ranar Talata a Legas yayin wani taron bita na kwana daya kan rahoton laifukan kudi da hukumar ta shirya wa wasu ‘yan jarida.

 

Shugaban wanda ya yi magana da mahalarta taron ta hanyar ta yanar gizo, ya ce hukumar ta yi farin ciki da kuma alfahari da kama irin wadannan laifuffuka, yana mai jaddada cewa hukumar ta himmatu wajen kara kamawa da yanke hukunci.

 

Ya ce hukumar ta kwato kadarorin da suka haura biliyoyin naira da dama.

 

Shugaban hukumar ya bayyana cewa an shirya taron bitar ne domin kara bunkasa da aikin jarida tare da baiwa mahalarta musamman wajen bayar da rahoton laifukan kudi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci