OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Hukumar Civil Defence Ta Kama Wani Da ATM 14, Da Layin Waya 22 a Kano

Hukumar Civil Defence Ta Kama Wani Da ATM 14, Da Layin Waya

Photo Source: Infoguide Nigeria

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya, NSCDC, ta kama wani matashi mai suna Ahmad Abdussalam mai shekaru 22 da katin ATM 14 da layin waya 22 a jihar Kano.

An kama Abdussalam ne da laifin mallakar layi Airtel guda 22 ba bisa ka'ida ba, yayin da yake amfani da katin ATM na bankin Fidelity guda 14 dauke da sunaye daban-daban.

Kwamandan hukumar NSCDC na Jihar, Adamu Zakari ne ya bayyana hakan a Kano.

Zakari ya ce wanda ake zargin yana yaudarar mutane a karkara da bude musu asusu yayin da suke sayar masa da katin ATM akan kudi N300 kowanne.

Ya kara da cewa jami’an hukumar sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake bakin aiki a lokacin da yake kunna wasu katunan ATM a bankin Fidelity a ranar Asabar, 12 ga watan Maris na 2022.

Zakari ya bayyana cewa, “Mutanen mu sun kama Abdussalam ne kuma bai iya bayar da gamsasshen bayanin asusun bankin ba dangane da katinan ATM guda 14 da aka samu a hannunsa.

“Da aka yi masa tambayoyi, sai ya hada mu da wani Umar Surajo wanda ya ce shi ne ya shirya wannan aika-aika.

“Bayan an yi masa tambayoyi, Abdussalam ya amsa cewa Umar Surajo ne ya gabatar da shi kuma ya dauke shi aiki inda ya umarce shi da ya je banki ya kunna katunan a na’urar ATM.”

Kwamandan ya kara da cewa an kama wani wanda ake zargi mai suna Muhammad Ali, wakilin kamfanin na Airtel da laifin hada kai wurin aikata laifin.

“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa an samu wadannan katunan ATM ne daga mutanen kauyukan da ba su da laifi, wadanda ba su san illar sayar da katin nasu na ATM ba,” ya bayyana.

Don haka ya ja kunnen jama’a da su guji sayar da katinan su na ATM, ya kara da cewa ana amfani da irin wadannan katunan wajen aikata laifukan kudi irin na ta’addanci.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci