OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Hukumar Hisbah Ta Kama Kwalaben Giya 5,800 A Kano

Hukumar Hisbah Ta Kama Kwalaben Giya 5,800 A Kano

Giya

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta ce ta kama wasu motoci uku makare da kwalaben giya.

 

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah, Haruna Ibn-Sina shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a garin Kano yayin da yake duba motocin da aka kama a ofishin na Hisbah.

 

Kakakin hukumar, Lawan Fagge, ya bayyana cewa an kama motocin ne a ranar Lahadi.

 

An kama Mota kirar Mercedes Benz, mai dauke da kwalaben giya 1,800; sai karamar motar Sienna, dauke da kwalaben giya 3,000 sai kuma motar Golf Volkswagen dauke da kwalaben giya 1,000.

 

Fagge ya bayyana cewa, Ibn-Sina ya yabawa sashin hana shan maye da suka damke motocin bisa kokarinsu na ganin an hana shan barasa da muggan kwayoyi a jihar.

 

Shugaban sashin hana shan kaya maye, Jamilu Hassan-Yakasai, ya bayyana cewa an kama motoci guda uku ne a lokacin da suke kokarin shigar da barasa cikin garin Kano.

 

Shugaban Hukumar ya tabbatar da cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo sauyin kauda duk wani naui na miyagun dabiu, musamman masu safarar miyagun kwayoyi da kuma taammali da miyagun kwayoyi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci