OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Harin Ta'addanci: Amurka Ta Umarci Jami'anta Dake Abuja Su Koma Gida

Harin Ta'addanci: Amurka Ta Umarci Jami'anta Dake Abuja Su K

Ƙasar Amurka ta buƙaci ma'aikatanta da ƴan uwansu mazauna Abuja da su fice su koma gida.

Wannan na zuwa ne yayin da ake fuskantar barazanar ta'addanci a babban birnin Najeriya, Abuja da kuma manƴan birane a ƙasar.

Wannan yana ƙunshe ne a cikin sabuwar sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar.

Daga cikin ƙasashen da suka yiwa ƴan ƙasashensu gargaɗi sun haɗa da Birtaniya, Canada, Australia, Ireland, Denmark, Bulgaria, Indiya da Jamus.

Anata ɓangaren Gwamnatin Tarayya ta tabbatar wa ƴan Najeriya cewa babban birnin ƙasar lafiya lau yake kuma babu barazanar harin ta'addanci.

Duk da wannan tabbacin, an samu rahotannin da ba a tabbatar da su ba na cewa baki ƴan ƙasashen waje sun fice daga ƙasar.

Amurka ta fitar a cikin wata sanarwa cewa a shirye take ta kwashe ƴan ƙasarta daga Najeriya saboda fargabar harin ta'addanci.

"Muna ba da shawarar cewa ƴan Amurka kada su yi tafiya zuwa Abuja a wannan lokacin.  

"Bugu da ƙari, a ranar 27 ga Oktoba, 2022, ma'aikatar ta ba da umarnin ficewa daga cikin iyalan ma'aikatan gwamnatin Amurka dake Abuja, sakamakon ƙaruwar hare-haren ta'addanci, biyo bayan izinin da aka ba wa ma'aikatan gwamnatin Amurka.

“Ofishin jakadancin Amurka a Abuja yana iya ba da agajin gaggawa ga ƴan ƙasar Amurka a Abuja kawai.  

"Babban ofishin jakadancin Amurka da ke Legas yana ba da duk wani aiki na yau da kullun da na gaggawa ga ƴan kasar Amurka a Najeriya, cewar Jaridar Daily Trust. 

Sanarwar ta ƙara da cewa "Jama’ar Amurka a Najeriya da ke buƙatar taimako su tuntubi [email protected] ko +234 1 460 3410.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci