OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Harin Goronyo: Buhari Ya Sha Alwashin Dakile 'Yan Bindiga

Harin Goronyo: Buhari Ya Sha Alwashin Dakile 'Yan Bindiga

Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha alwashin dakile 'yan bindiga da kuma tura musu gargadi mai tsauri.

Yayin da yake gargadin, yace 'yan bindigan su sani cewa lokacin hallakar su ta iso kana su sani basu da wurin buya.

Shugaba Buharin ya bayyana haka ne lokacin da yake maida martani kan harin da aka kai wata kasuwa dake karamar hukumar Goronyo dake jihar Sakkwato.

Harin da aka kai a ranar Lahadi ya jawo rashin rayuka fiye da 30.

Babban Mataimakin Shugaban na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Garba Shehu ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa ga manema labarai.

Shugaba Buhari ya ce lokacin da 'yan bindigan suke cin karen su ba babbaka ya kawo karshe musamman yadda maikatan tsaro na Najeriya suka samu karin kayan yaki. 

Yayin da shugaban yake mika ta'aziyar sa ga iyalen wanda harin ya rutsa da su, ya roki 'yan Najeriya cewa kada su rusuna da gwamnati domin Gwamnatin ta kara himma wurin kare jama'a.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci