OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Da Osinbajo Zasu Kashe Biliyan 11.92 Wajen Tafiye-Tafiye

Buhari Da Osinbajo Zasu Kashe Biliyan 11.92 Wajen Tafiye-Taf

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo za su kashe Naira biliyan 11.92 wajen tafiye-tafiyen gida da waje da kuma gyaran jiragen saman shugaban kasa.

 

 Adadin da aka ambata ya kuma hada da Naira biliyan 1.58 da aka ware domin gyaran jiragen saman Shugaban kasa da Naira biliyan 1.60 da aka ware domin gyaran injinan jiragen Gulfstream GV da CL605.

 

A hannu guda kuma, ‘yan majalisar dokokin kasar za su samu Naira biliyan 100 domin gudanar da ayyukan mazabu, wadanda a cewar hukumar yaki da rashawa ICPC ta Dade tana zargin hanyar aringizon kudaden Al'umma ce zalla.

 

Idan za'a iya tunawa a ranar Juma’ar data gabata ne shugaba Buhari ya gabatar da kudirin kasafin kudi na Naira 20.51. tiriliyan na kasafin shekarar 2023 ga Majalisar Dokoki ta Kasa.

 

Kasafin kudin ya kai kusan Naira biliyan 750 sama da Naira Tiriliyan 19.76 da aka gabatar a shekarar data gabata.

 

 Gwamnatin za ta kashe Naira miliyan 250 wajen samar da mai na jiragen saman.

 

Hakazalika, sayan kayan zirga-zirga da tsaron jiragen sama zai dauki Naira biliyan 1.50, sannan za ayi amfani da Naira miliyan 650 wajen gina sabon filin saukar jirage masu saukar ungulu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci