OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Buhari Ya Tafi Ƙasar Koriya Ta Kudu Don Halartar Taron Duniya Kan Harkar Lafiya

Buhari Ya Tafi Ƙasar Koriya Ta Kudu Don Halartar Taron Duni

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa birnin Seoul na ƙasar Koriya ta Kudu domin halartar taron duniya na farko na shekarar 2022.

Buhari zai tashi yau Lahadi daga Abuja wanda Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban ƙasar ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Taron na kwanaki biyu mai taken: “Makomar Allurar rigakafi da Kiwon Lafiyar Halitta,” gwamnatin Jamhuriyar Koriya da Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ne suka shirya shi.

Adesina ya ce an gayyaci Najeriya zuwa taron ne bisa zaɓin ta da wasu ƙasashen Afirka biyar da hukumar lafiya ta duniya da Tarayyar Turai, EU suka yi.

A cewar sa wasu da ake sa ran za su fito a taron kolin halittun na duniya su ne shugabannin kamfanonin rigakafi na duniya da kuma kamfanonin nazarin halittu.

Ya ƙara da cewa shugabannin za su tsara ra'ayoyi don ganin cewa "Tsaron kiwon lafiya na duniya ya dogara sosai kan ƙirƙire-ƙirƙire da cigaban masana'antar halittu.

Ya ce ana sa ran Buhari zai gabatar da jawabi a taron, sannan kuma ya keɓe da shugaban ƙasar Koriya ta Kudu Yoon Suk-yeol.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa shugaban na Najeriya zai samu rakiyar Gwamna Aminu Bello Masari da Sani Bello na jihohin Katsina da Neja.

Sauran sun haɗa da Geoffrey Onyeama, Osagie Ehanire da Adeniyi Adebayo, ministocin harkokin waje, kiwon lafiya, masana'antu, kasuwanci da zuba jari, a jere;  da Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur.

Sauran kuma sune, Babagana Monguno, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro;  Ahmed Abubakar, Darakta Janar na Hukumar Leken Asiri ta ƙasa;  Moji Adeyeye, Darakta Janar na NAFDAC da Ifedayo Adetifa, Darakta Janar na NCDC.

Sauran da ke cikin tawagar sun haɗa da: Bashir Jamoh, Darakta Janar na NIMASA;  Abike Dabiri-Erewa, shugaba, NiDCOM da sauran manyan jami'an gwamnati.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci