OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnonin Arewa-maso-Gabas Sun Koka Kan Kwararar Da Ƴan Bindiga Ke Yi Zuwa Yankin

Gwamnonin Arewa-maso-Gabas Sun Koka Kan Kwararar Da Ƴan Bin

Shugaban Gwamnonin Arewa maso Gabas, Babagana Umara Zulum of Borno State

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa maso Gabas sun ce yawaitar ƴan bindiga da suka fice daga yankin Arewa-maso-Yamma ya sanya zaman lafiya a yankin ya yi rauni.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a daren Juma’ar da ta gabata a cikin sanarwar wanda Gwamnan Jihar Yobe Mai Buni ya karanta, mai dauke da sa hannun Shugaban kungiyar Arewa maso Gabas Farfesa Babagana Zulum, Gwamnan Jihar Borno.

A cewar su, an samu alaka tsakanin ayyukan haƙar ma'adinai da rashin tsaro, tare da jaddada bukatar bin ka'idojin amfani da filaye.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Ƙungiyar ta yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jami’an tsaro bisa kokarin da ake na yaki da ƴan Boko Haram.  

"... an samu ingantuwar yanayin tsaro a yankin wanda akasari aka samu ta hanyar daukar matakai na musamman.

"Ƙungiyar ta lura da zaman lafiya da ake samu a yankin, musamman yadda ake samun raguwar rigingimun rikicin manoma da makiyaya, a matsayin abin ƙarfafawa. 

"Sai dai kuma ana samun ƙaruwar matsalar rashin tsaro a yankin sakamakon yawaitar ƴan bindigar da sannu a hankali jami’an tsaro ke fatattakar su daga yankin Arewa maso Yamma.  

"Dangane da kwararowar ƴan bindigar, akwai bukatar a kaddamar da taswirar tsaro ta hadin gwiwa tare da hukumomin tsaro da gwamnatin tarayya.

Gwamnonin jihohin Adamawa, Bauchi, Borno Gombe, da Yobe sun hallara a Gombe yayin da jihar Taraba da ta samu wakilci a taron da aka gudanar a Gombe, in ji jaridar Punch.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci