OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Najeriya Na Asarar Gangar Danyen Mai 700,000 a Kullum Saboda Barayi – Minista

Najeriya Na Asarar Gangar Danyen Mai 700,000 a Kullum Saboda

Karamin ministan albarkatun man fetur Timipre Sylva  yace Najeriya na asarar akalla gangar danyen mai 700,000 ga barayi a kullum.

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen yaye daliban Cibiyar Koyar da sanin Man Fetur, PTI.

Ministan, wanda ya samu wakilcin Gabriel Aduda, babban sakatare a ma’aikatar albarkatun man fetur, ya ce gwamnatin tarayya na yin hadaka domin dakile wannan matsalar.

Ya ce satar danyen mai yana yin illa ga harkan kudaden waje na kasar, cewar Jaridar Daily Nigerian.

“Satar mai na hana kasar samun gangar danyen mai kusan 700,000 a kowace rana.  

"Mummunan illar hakan shi ne raguwar samar da danyen mai da raguwar kudaden shiga na kasa,” inji shi.

Ya ce ma’aikatar man fetur za ta hada kai da majalisar dokokin kasar domin tabbatar da cewa an ba da cikakkiyar kulawa ga gyaran dokar PTI.

Mista Sylva ya ce cibiyar za ta iya samun nasarori sosai idan aka yi wa dokar PTI kwaskwarima domin baiwa cibiyar damar samun karin kudade.

Mista Sylva ya taya daliban da suka kammala karatun murna tare da ba su tabbacin cewa akwai damammaki a harkar man fetur da iskar gas.

"Kwarewar da kuka samu za ta kasance mai mahimmanci wajen tabbatar da ci gaban manufofin da ake samu a masana'antar mai da iskar gas.

"Ina faɗin hakan da kwarin gwiwa saboda har yanzu duniya ta dogara da iskar gas," in ji shi.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci