OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnatin Kaduna Ta Ba Da Umurnin Karfafa Doka Kan Barace-barace Da Talla

Gwamnatin Kaduna Ta Ba Da Umurnin Karfafa Doka Kan Barace-ba

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufa'i| Hoto Daga: BBC

Aranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin jihar Kaduna ta bada umurnin tabbatar da tsauraran dokokin ci gaba da hana Almajirai, barace-barace da talla a jihar.

A cikin wata sanarwa daga gidan gwamnati, Gwamnatin ta tunatar da “dukkan mazauna jihar cewa jihar na da dokokin kare yara da hana barace-barace kan tituna da talla."

Sanarwar ta ce, gwamnati ta umurci jami’an da ke tabbatar da bin dokan da aka saka na kwanan nan da suka hada da dokar hana babura, cewa su hada da daukar matakin yaki da cin zarafin yara, barace-barace da kuma talla.

Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Jihar da su baiwa jami’an hadin kai domin aiwatar da dokokin da suka dace, kana jama'a su kiyaye bin doka da oda.

Zaku iya tuna cewa gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa'i a karon mulkin sa na farko ya aiwatar da bada ilimi kyauta ga yara don kula da matsalar cin zarafin su. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci