OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Mako da ya shude

Gwamnatin Kano ta magantu kan batun harsashin daya harbi Dan jarida a gidan gwamnatin

Gwamnatin Kano ta magantu kan batun harsashin daya harbi Dan

Governor Abba Kabir Yusuf

Gwamnatin jihar Kano ta musanta labarin dan jaridar gidan talabijin na ARTV da harsashi ya same shi a gidan gwamnati a daren Juma’a.

Allnews.ng ta ruwaito cewa, wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin na Abubakar Rimi, a gidan gwamnatin Naziru Idris Ya’u, ya sami rauni sakamakon harbin bindiga a yammacin ranar Juma’a, a gidan gwamnati.

Ba a San dai ta inda akai harbin ba, Amma tuni aka garzaya da dan jaridar da ya jikkata zuwa asibitin gidan gwamnati.Sai dai a cikin wata sanarwa da Sanusi Bature Dawakin Tofa, Mai Magana da yawun gwamnan jihar , ya fitar a ranar Asabar, ya musanta faruwar lamarin inda ya bayyana shi a matsayin labari mara tushe.

Sanarwar ta kara da cewa, “An jawo hankalin gwamnatin jihar Kano kan wani rahoton daya fito daga kafafen yada labaran yanar gizo da ke nuna cewa wani harsashi ya sani wani dan jarida dake wakiltar gidan talabijin din ARTV a gidan gwamnatin jihar.magana ta gaskiya, Naziru Yau, wakilin gidan talabijin na jiha, babu wani harsashi da ya same shi”.

‘’Maimakon haka, ya samu raunuka daga tarkacen karfunan da ake fito da su daga wani gini da ake gyara a gidan gwamnatin jihar Kano.

"Ina dada jaddada cewa ya kamata ‘yan jarida su ringa taka-tsan-tsan yayin da suke gudanar da ayyukansu, musamman a wuraren da ayyukan gine-gine ka iya haifar da hadari. 

"Don haka muna watsi da duk wani jita-jita tare da jaddada mahimmancin bayar da rahoto mai kyau da kuma cikakken bincike don magance yada labarai marasa tushe" in ji sanarwar.

Sanarwar ta kuma kara tabbatar wa al’umma kudurin gwamnati na tabbatar da tsaron duk wani mutum da ke cikin harabar gidan gwamnatin da kuma jihar baki daya. 

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci