Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya kaddamar da shirin tsaftar muhalli a duk wata a fadin jihar domin tabbatar da tsafta da lafiyar alummar Jihar.
Gwamnan ya amince da ranar Asabar din karshen kowane wata don gudanar da aikin tsaftar muhallin da zai fara aiki daga watan Afrilun da muke ciki.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan albarkatun ruwa da muhalli da gandun daji Mohammed Sa'idu Fawu a ranar Talata, ta rawaito gwamnan ya amince da cewa za a gudanar da aikin tsaftar muhallin ne tsakanin karfe 8:00 na safe zuwa 10:00 na safe.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “A bisa kudirin gwamnati na samar da tsaftar muhalli mai dorewa, Mai Girma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya CON (Dan Majen Gombe), ya amince da gudanar da ayyukan tsaftar Muhalli a duk wata. Yayin aikin tsaftar muhalli a jihar za'a dakatar da zirga-zirgar alumma tun daga fara aikin tsaftar harzuwa kammala shi a duk ranar Asabar na karshen kowane wata, masu aikin agaji ne kadai aka yarda suyi Kai kawo yayin tsaftar muhallin"
Har ila yau, an umurci dukkan ma'aikatu da sauran jama’a da su yi biyayya ga wannan umarni domin tawagar jami’an ma’aikatar albarkatun ruwa, muhalli da gandun daji da kuma hukumar kula da tsaftar muhalli ta jihar Gombe (GOSEPA) za su sanya ido sosai don tabbatar da an gudanar da tsarin yanda ya kamata.
0 Tsokaci