OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Za'a Iya Amfani Da Ragowar Kayan Miya Wajen Samar Da Iskar Gas Din Girki —Suleiman Gidado

Za'a Iya Amfani Da Ragowar Kayan Miya Wajen Samar Da Iskar G

Gawayi, shi ne makamashin da yanzu mafi yawan ƴan Najeriya ke amfani da shi wajen girke girke

A hutun ƙarshen makon nan ne aka jiyo Kungiyar masu sana’ar gawayi da safararsa zuwa kasashen ketare, wato ‘National Association of Charcoal Producers, Dealers, Exporters Association of Nigeria’, tace akwai bukatar masu samar da gawayi su rage sare itatuwa ba tare da maye gurbinsu ba.

Shugaban kungiyar, Tunde Ede, da yayi kiran a Minna babban birnin jihar Neja, ya ce akwai bukatar yawaita shuka sababbin bishiyoyin da zasu maye gurbin wadanda ake sarewa domin samar da gawayin da ake girki da shi.

Sai dai ɗaya daga masu rajin kare muhalli a Kano, Suleiman Gidado Isma’il, abu mafi soyuwa shi ne a daina sare bishiyoyin.

Yace akwai hanyoyin samar da makamashi kamar ta hanyar amfani da ragowar kayan miya, da wasu dabaru domin samar da tsaftataccen gas na makamashin girki.

Suleiman Gidado, ya kuma kara da cewa, hanyoyin samar da irin wannan makamashin gas masu tsafta basu da wahala sosai matukar aka samu tallafin da ya dace.

Ya ce duk da cewa yanzu haka babu wata kungiya dake samar da irin wannan a Kano, sun taba horar da matasa yadda zasu samar da makamashin amma basu fitar da batun ta fuskar kasuwanci ba.

Yanzu haka dai, mafi akasarin ƴan Najeriya sun fi amfani da gawayi wajen girke girke don saukin sa idan aka kwatanta da iskar gas ko kalanzir.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci