OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Watanni da suka shude

Inuwa Yahaya Ya Taya Sabon Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Murnan Lashe Zaɓe

Inuwa Yahaya Ya Taya Sabon Shugaban Ƙungiyar Ɗalibai Murna

Comrade Usman Umar Barambu

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya taya sabon zababben shugaban kungiyar dalibai ta kasa (NANS), Kwamared Usman Umar Barambu murnar nasarar lashe zaɓe.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ya fitar ta bakin Darakta Janar na yaɗa labarai na gidan gwamnati Ismaila Uba Misilli a Gombe.

Inuwa ya ce nasarar da Barambu ya samu ta sa shi farin ciki kasancewarsa dalibi na farko daga jihar Gombe da aka zaba a matsayin shugaban ɗalibai.

Gwamnan ya bayyana tsohon shugaban kungiyar daliban jihar Gombe ta kasa (GOSSA) a matsayin matashi mai kishi kuma jajirtacce kuma mai kyawawan halaye na shugabanci, inda ya bukace shi da yayi amfani da kwarewar sa wajen kawo sauyi a kungiyar domin amfanin daliban Najeriya.

Sai dai ya dora masa alhakin ci gaba da kawo  daukaka a jiharsa ta haihuwa.

Gwamnan ya ba shi tabbacin goyon baya, hadin kai da kuma fatan alheri daga gwamnati da al’ummar jihar Gombe a yayin da yake jagorantar kungiyar daliban Najeriya.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci

shahararrun labarai