OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gwamnatin jihar Gombe ta amince da kashe N10bn domin ayyukan titunan cikin Gari Da Sauran su

Majalisar zartaswar jihar Gombe karkashin jagorancin gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya ta amince da kashe naira biliyan 10 domin gudanar da ayyukan tituna.

Majalisar ta amince da Naira biliyan 8.8 don gina titunan cikin gari guda 17.

Majalisar ta kuma amince da wani Naira biliyan 1.2 domin gyaran gaggawa na hanyoyin da ambaliyar ruwa ta lalata su. 

Kwamishinan Ayyuka da Sufuri, Engnr. Abubakar Bappah ne ya bayyana wa manema labarai hakan jim kadan bayan kammala taron a ranar Litinin.

Bappah ya ce za a gina titunan garin guda 17 ne a Kagarawal, Pantami/Gabukka, tsohuwar GRA da ofishin hukumar kula da ma’aikata zuwa makarantar kimiyya ta Gombe (science two) ya hada da yankunan Shongo da sauransu.

Majalisar ta kuma dage haramcin da aka yi wa Makarantun aikin kiwon lafiya masu zaman kansu 7 daga cikin 17 da aka rufe saboda matsalar lasisi da kayan karatu.

A cewar shugaban kwamitin da ke kula da dorewar Makarantun Kiwon lafiya masu zaman kansu, Barista Zubair Muhammad Umar, cibiyoyi 7 din sun hada da Fountain College of Health Science and Technology Tunfure, Kwalejin Conformance of Health Science and Technology Billiri, Garkuwa College of Health Science and Technology Gombe , Lamido College of Hygiene Liji, Ummah College of Health Science and Technology, Dukku, International College of Health Science and Technology, da Haruna Rasheed College of Health Science and Technology Dukku.

Sai dai sauran makarantun da har yanzu aka dakatar da su sun hada da Ilimi College of Health Science and Technology Gombe, Barunde College of Health Science Kumo, Legacy College of Health Science and Technology Gombe, College of Health Science Filiya, College of Health Science Deba da Bormi College of Health Sciences and Technology Bajoga.

Sauran sun hada da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya ta Bajoga, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Bambam, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Lafiya ta Kwami da Kwalejin Kimiyyar Lafiya Lalaipido.

Kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gwamnan, Ismaila Uba Misilli ta nuna, “Barista Zubairu Umar, wanda shine babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar yace matakin da gwamnati ta dauka akan lamarin shine na tantance kwararrun ma'aikata ba wai kame saboda adawa ba. 

“Yayin da yake mai da hankali kan matsayin shugaban don tabbatar da dorewar Makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu a jihar, Kwamishinan Lafiya, Dokta Habu Dahiru ya ce hakan ya kasance wani bangare na shawarar gwamnati na tabbatar da lafiya da inganci sa ne a jihar.”

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci