OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 2 Shekaru da suka shude

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2022 Ga Majalisar Jaha

Gwamnan Gombe Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2022 Ga Majalisar

Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya yayin da yake gabatar da kasafin kudi na 2022.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya gabatar da kasafin kudi na naira biliyan 154.6 na shekarar 2022.

Gwamnan ya gabatar da kasafin ne a ranar Alhamis a zauren majalisar dokokin jihar.

Yahaya ya bayyana cewa kashi 44.7 (N69.1billion) na kasafin kudin na kashewa akai-akai ne yayin da kashi 55.3 (N85.4billion) aka ware domin manyan ayyuka.

Ya bayyana cewa an kammala kashi 69 na kasafin kudin 2021 wanda aka kiyasta a kan Naira biliyan 120.

Ya kuma bayyana cewa kasafin kudin shekarar 2022 shi ne na farko da zai cika shirin ci gaban jihar na shekaru 10 da gwamnatinsa ta tsara.

Yayin da yake lura da irin goyon bayan da gwamnatinsa ta samu daga majalisar, ya yaba wa ‘yan majalisar “a tafiyar da muka yi na daukar jihar Gombe zuwa mataki na gaba”.

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Abubakar Mohammed Luggerewo ya bayyana jin dadinsa kan gabatar da kasafin kudin a kan lokaci.

Ya yaba wa gwamnan kan yadda yake gaggauta aiwatar da dokokin da majalisar ta shigar wanda suka shafi jama'an su.

Ya kuma ba da tabbacin cewa majalisar za ta tattauna kan kasafin tare da la'akari da cigaban al'umma.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci