Kasar Amurka da Birtaniya sun gargadi ‘yan kasarsu mazauna Najeriya kan hare-haren ta’addanci a kasar musamman a Abuja babban birnin tarayya.
A cewar wani mai ba da shawara kan harkokin tsaro na ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya ce akwai yiwuwar a kai “munanan hare-haren ta’addanci a Najeriya, musamman a garin Abuja.”
Ofishin ya ce wuraren da ake kaiwa hari na sun haɗa da gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni, manyan kantuna, otal-otal, mashaya, gidajen cin abinci, wuraren wasannin motsa jiki, tashoshin sufuri, wuraren tabbatar da doka da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Sakamakon haka, ofishin jakadancin Amurka ya ce, za ta rage zirga zirgan ta na ayyuka har sai nan gaba.
Ta shawarci Amurkawa da ke Najeriya da su guji duk wani tafiye-tafiye ko yawo mara muhimmanci, su kasance idon su a bude, su guje sa cunkoson jama'a, da bin labaran cikin gida da kuma neman shawarwarin hukumomin tsaro.
Bugu da kari,Ofishin jakadancin ta shawarci Amurkawa mazauna Najeriya da su sake duba tsare-tsaren tsaron kansu, su rika cajin wayar salulan su saboda lamarin gaggawa in ya taso da kuma daukar shaidar da ta dace.
Haka itama Babbar Hukumar Burtaniya ta bayar da irin wannan shawara ga yan kasar ta mazauna Najeriya .
0 Tsokaci