OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Wakilin kasar Ukraine ya shawarci daliban Najeriya da su yi watsi da tayin kasar Rasha

Wakilin kasar Ukraine ya shawarci daliban Najeriya da su yi

Ƙasar Ukraine ta ​​​bukaci dalibai yan Najeriya da kada su karbi tayin kasar Rasha saboda ita ta yi sanadin kawo musu cikas a karatun su.

 

A wata da jakadan Ukraine, Maksym Subhk ya yi da jaridar Premium times,yace  yace ba daidai ba ne ɗaliban Najeriya waɗanda yaƙin Ukraine ya dakatar da karatun su su yadda su karbi gurbin karatu a kasar Rasha.

 

Wakilin kasar Ukraine din ya bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kawo Najeriya.

 

Ya kara da cewa " a ɗabi'a hakan ba daidai ba ne.

 

Dubban daliban Najeriya da ke karatu a kasar Ukraine sun sami datsewar karatunsu sakamakon mamayar da kasar Rasha ta kai wa Ukraine. An kashe daruruwan mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu tun lokacin da aka fara yakin a cikin watan Fabrairu.

 

Ya ce daliban da abin ya shafa sun zama masu kishin kasa na Najeriya da kuma Ukraine tunda sun san musabbabin abinda ya haddasa yakin.

 

Ya ce Ukraine na kokarin ganin ta samowa dalibai wasu hanyoyin da za su iya ci gaba da karatunsu, ciki har da kasashen da ke makwabtaka da su.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci