OTHER SERVICES

Connect with us

  • Hausa News
  • Updated: 1 Shekara da ya shude

Gombe : Dan majalisa mai wakiltar mazabar Akko zai gina makarantu, da asibiti cikin makonni 6

Gombe : Dan majalisa mai wakiltar mazabar Akko zai gina maka

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Akko a jihar Gombe, Usman Bello-Kumo, ya bayar da kwangilar gina makarantu da asibitin haihuwa na zamani cikin makonni shida a mazabarsa.

Mista Kumo wanda shi ne shugaban kwamitin majalisa kan harkokin ‘yan sanda, ya bayyana hakan ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin bikin kaddamar da ayyuka a Tumfure da Unguwan Baka a gundumomin Gona da Pindiga na karamar hukumar Akko ta jihar.

Dan majalisar wanda ya samu wakilcin Abubakar Luggerewo, kakakin majalisar dokokin jihar Gombe, ya ce za a gina asibitin haihuwa na zamani tare da kaddamar da shi cikin makonni 6.

A cewarsa, asibitin mai daukar gadaje 45 za a samar da isassun kayan aiki na zamani don samun ingantaccen kiwon lafiya.

A garin Pindiga, yayin da yake kaddamar da aikin gina makarantar firamare a Unguwan Baka, dan majalisar ya ce za a gina ajujuwa 6, ofisoshin malamai da kantin sayar da kayayyaki don inganta karatun yara a cikin al'umma.

Dan majalisar ya kara da cewa matakin zai tabbatar da ganin an rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a mazabar.

A gundumar Akko, yayin da yake duba aikin gina ajujuwa 3 a Akkoyel, dan majalisar ya kuma bayar da sabuwar kwangilar gina makarantar Islamiyya a unguwar Barambu.

Batu

Join our Telegram platform to get news update Join Now

0 Tsokaci